Hausa da Hausawa
Hausa dai harshen magana ne wanda ake amfani da shi a kasashen Afirka ta Yamma da kuma wasu kasashen na Afirka ta tsakiya. Alkalumma sun nuna cewar mutane kimanin milyan 20 ne suke magana da harshen hausa a matsayin harshen uwa. sauran milyan 5 biyar kuma suna amfani da shi a matsayin harshensu na harkokin yau da kullum. Idan aka yi la'akari da Tarihin Hausawa za a ga cewar kasar Hausa ta samo asali ne daga arewacin Najeria da kuma kudancin Nijar kuma sai ta bunkasa i zuwa sauran kasashen Afirka ta yamma kamar Ivory coast, Gana, Sudan, Benin, Gine, Afirka ta tsakiya da sauransu ta hanyar kasuwanci da sauye sauyen tsarin al'umma.